ABNA24 : Ministan harkokin wajen kasar ta Turkiya ya fada a jiya juma’a cewa; ci gaba da amfani da harshen kakaba takunkumi ba mai amfani ba ne, kuma ya zama wajibi ga kungiyar tarayyar turai din ta fahinmci cewa irin wannan matakin ba inda zai kai ta.”
Kungiyar tarayyar turai dai ta gargadin kakaba wa Turkiya takunkumi, idan har ta ci gaba da hako makamashi a ruwan tekun meddittranea da ake da sabani akansa.
Kasashen Turkiya, Girka da kuma Cyprus suna da sabani da juna akan wacce take da hakkin hako makamashi a gabashin tekun Mediterrania.
Sai dai an sami koma bayan zaman dar-dar da ake da shi a yankin, bayan da kasashen Turkiya da Girka su ka amince da su zauna kan teburin tattaunawa.
342/